Mutane 13 sun rasa rayukansu yayinda wasu 2 suka bata sakamakon kifewar jirgin ruwan kwale-kwale a kogin Albert da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Jami'in gudanarwar yankin Mahagi, Ukumu Pierre Klaver ya fadi cewar jirgin ya kife sakamakon kadawar iska mai karfi kuma mutane 13 sun mutu.
Sanarwar ta ce akwai mutane 17 a cikin jirgin, an kubutar da 2 inda wasu suka bata kuma ana ci gaba da neman su.
A kogin Albert ana yawan samun kifewar jiragen ruwan kwale-kwale saboda rashin ingancinsu da kuma daukar mutane sama da yadda ya kamata.