Kwalara ta yi ajalin mutane 37 a Najeriya

Kwalara ta yi ajalin mutane 37 a Najeriya

Mutane 37 ne suka rasa rayukansu a tsawon wata dayan da ya gabata sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya.

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko na jihar Bauchi Dr. Rilwan Muhammad ya shaida cewa, daga ranar 25 ga Mayu zuwa yanzu mutane 1,799 ne suka kamu da cutar a yankunan jihar daban-daban.

Muhammad ya shaida cewa, mutane 17 sun sake mutuwa wanda ya kawo adadin wadanda cutar ta kwalara ta kashe zuwa 37.

Muhammad ya kuma ce, an aike da magunguna da kayan bayar da agajin gaggawa zuwa ga yankunan da cutar ta bulla, an kuma bukaci jama'a da su dauki matakan hana cutar yaduwa.


News Source:   ()