Mutane 146 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya.
Sakatare Janar na Asibitin Sir Yahaya Aminu Bunza ya shaida cewa, bayan bullan kwalara a yankin Sakaba na jihar, ta bulla a karin jihohi 20.
Bunza ya ce, mutane dubu 2,028 cutar ta kama a jihar Kebbi yayinda 146 daga ciki suka mutu.
Gwamnati ta aika da magunguna da sauran kayan kula da lafiya a yankunan da cutar ta yi tsamari, an kuma yi kira ga jama'ar yankunan da su kula sosai.
Bunza ya yi kira ga ma'aikatan lafiya da su kauracewa duba masu dauke da cutar a gida, kuma lallai duk wanda aka samu ya kamu to a garzaya da shi asibiti mafi kusa.