'Yan Najeriya kusan dubu 100 ne suka yi gudun hijira daga yankunansu zuwa kasar Nijar don neman mafaka sakamakon hare-haren 'yan ta'addar Boko Haram a arewa maso-gabashin kasar.
Labaran da jaridun Najeriya suka fitar sun rawaito wani jami'in gwamnati da ya nemi a boye sunansa na cewa, 'yan ta'addar Boko Haram sun kai hare-hare a ranakun 13 da 14 ga Afrilu a yankin Damask na jihar Borno.
Jami'in ya ce, sakamakon hare-haren, a cikin kwanaki 2 kusan mutane dubu 100 ne suka gudu zuwa Jamhuriyar Nijar.
Haka zalika ya kara da cewa, an kona gine-ginen da suka hada da na gwamnati da shaguna da dama a yayin kai hare-haren.
A Harin da 'yan ta'addar suka kai a ranar Laraba a Damask sun kashe mutane 10.