Firaministan Gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya, Abdulhamid Dbeibah da ya ke bayyana cewar dukkan bangarori sun bukaci Ma’aikatar Tsaro ya ce, "Ba za mu yarda da wani yakin ba. Dole ne yakin ya tsaya."
Majalisar Wakilai ta halarci taro a garin Sirte don kada kuri'ar amincewa da gwamnatin Dbeibah, wanda aka zaba a matsayin Firaminista a taron da aka gudanar kan tattaunawar siyasar Libiya da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta jagoranta.
Dbeibah wanda ya gabatar da shirin gwamnatinsa ga Majalisar ya ce,
"Duk bangarorin suna son Ma'aikatar Tsaro. Ba za mu iya barin wani yakin ba. Dole ne yakin ya tsaya."
Da yake bayyana cewar ya zabi Minista daya ne kacal a cikin gwamnatin kuma sauran an zabe su ne sakamakon shawarar mambobin Majalisar Wakilai, Dbeibah ya lura cewa an yanke shawarar cire sunayen mutanen da ke yawan yin jayayya a tsoffin gwamnati ne daga Majalisar Ministocin.
Dbeibah ya jaddada cewa akwai ministoci 26 a cikin ministocin nasa, bai san dukkansu ba amma ya dogara ga shawarwarin Majalisar.
Ya kuma jaddada cewa ba zai bar cin hanci da rashawa ba kuma duk ministocin zasu bayyana kadarorinsu.
Dbeibah da yake magana kan batun sojojin haya na kasashen waje a kasar ya ce “’yan Libiya na da wuka a bayansu" sannan ya kara da cewa ya kamata a tsarkake Libiya daga sojojin haya.
Kakakin Gwamnatin Hadin Kan Kasa, Mohammed Hammuda ya bayyana cewar a halin yanzu, Firaminista Dbeibah zai fara aiki a matsayin Ma'aikatar Tsaro da Ma'aikatar Cikin Gida a matakin farko kuma za a yi nadi ne a nan gaba tare da shawarwari da Majalisar Shugaban Kasa.
Majalisar Wakilai da ta taru a birnin Sirte na Libiya ta fara kada kuri’ar amincewa da Gwamnatin Hadin Kan Kasa karkashin jagorancin Firaminista Abdulhamid Dbeibah amma ta kara wa’adin da kwana daya yayin da aka kasa kammala zaman.