Rahotanni na nuni cewa an yi garkuwa da Atia Tilarious Azonhwi tare da wasu mutane uku, labarin da shugaban wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta gida da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya tuntuba a Bamenda.
Bugu da kari kuma, wani dan jarida, Patrick Thierry Ondoua, darektan jaridar "Le Point Hebdo", 'yan sanda sun kama tare da tsare su, a cewar wata sanarwar manema labarai daga kungiyar Editocin Jarida ta Duniya.
Garin Bamenda a Kamaru © Reinner Kaze / AFPAn kama dan jaridar ne da laifin almubazzaranci da dukiyar al’umma.
Taswirar kasar Kamaru © FMM Studio graphique"Har yanzu yana hannun 'yan sanda," Cyrille Kuete, shugabar kungiyar Editocin Jarida ta Duniya, ya shaida wa kamfanin dilancin labaren Faransa na a jiya Asabar.
Gwamnatin shugaba Paul Biya ta yi kakkausar ga duk wani nau'in adawar siyasa tun bayan da aka sake zabensa a karo na bakwai a shekara ta 2018.
Kuma tun bayan barkewar rikicin ‘yan aware a shekarar 2016 a yankuna biyu masu amfani da turancin Ingilishi na kasar, ana yawan yin garkuwa da mutane ba tare da neman kudin fansa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI