Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Musa Faki Muhammed ya yi kira ga hukumomin Amurka da su dauki matakan kawo karshen dukkanin dabi'ar nuna wariya a kasar.
Muhammed, ya fitar da wata sanarwa a rubuce inda ya ke tir da azabtar da wani bakin fata mai suna George Floyd da 'yan sandan garin Minneapolis dake Amurka suka yi, lamarin da ya yi sanadiyar rayuawrsa.
A yayinda yake tunatarwa akan matakin da kungiyar ta dauka a shekarar 1964 akan nuna wariyar da ake yiwa bakar fata a Amurka Muhammed ya kara da cewa,
"Ya zama wajibi ga jami'an Amurka su karfafa matakan kauda dukkanin dabi'ar nuna wariya na fata da kabilanci"
Muhammed, ya kuma nanata cewa Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi tir da Allah wadai akan ko wani irin nunawa bakar fata wariya.