Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta jitar a shafin farfagandanta jiya juma’a.
Harin wanda shine hari mafi muni da kasar ta fuskanta tun bayan shekarar 2021, an kaishi ne kan dakarun runduna yaki da ta’addanci ta Mirador dake aikin tabbatar da tsaro kan iyakan Nijar da kuma Burkina Faso.
Wasu manyan jami’an tsaro sun ce harin ya haddasa mumunar barna a bangaren sojoji yayin da ake cigaba da tattara bayanai daga wadanda suka ketare rijiya da baya.
kwanaki uku da afkuwa lamarin har yanzu gwamnati bata fitar da wasu alkalumma a hukumance dangane da adadin sojin da suka mutu a harin ba, amma kuma bagaren babban jam’iyar adawa ta ce Sojojin da aka kashe a yankin Alibori wanda ke kan iyakar Niger da Burkina Faso zasu iya kai 30.
A wata ganawa da manem alabarai, Shugaban kasar Patrice Talon, ya ce , ‘yan ta’adda na cigaba da cin karansu babu babbaka a iyakokin kasar kuma hakan ba karamin kalubale ne ga jami’an tsaron duk da irin kokarin da suke bayar wa.
A baya bayan nan dai Benin da makoftanta na yankin Sahel na fuskantar dinbim matsalolin tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI