Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ba ta yi kasa a gwiwa ba game da shawarar da ta yanke na dakatar da kasancewar Mali a matsayin mambar kungiyar duk da nadin Firaminista farar hula a rikicin siyasa.
A bayanin da ya gabatar a taron shugabannin kungiyar ECOWAS karo na 59, Jean-Claude Kassi Brou, shugaban kwamitin ECOWAS ya bayyana cewa nada firaminista farar hula a kasar Mali mataki ne mai kyau.
Da yake nuna cewa akwai kyawawan ci gaba a Mali, idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a yanzu Brou ya ce,
”Duk da haka, shugabannin ECOWAS sun yanke shawarar cewa ya kamata a sa ido a kan yanayin kafin a dage shawarar dakatar da Mali. Shugabannin na bukatar karin kwarin gwiwa kan ci gaban."