Kungiyar ba da agaji tace mutum 70 a fadan na kwanaki biyu a Sudan

Kungiyar ba da agaji tace mutum 70 a fadan na kwanaki biyu a Sudan

Ƙungiyar ba da agajin ta bayyanawa Kamfanin dillancin labarun Faransa cewa sojojin kasar ta Sudan,  sun yi  luguden wuta ta sama akan wani masallaci wanda ya yi  sanadin mutuwar mutum sama da 31 a ranar talata da ta gabata.

Hakazalika kungiyar ta zargi sojojin da amfani da manyan bama-bama wajen kai wannan harin da ya ɗaiɗaita mutane da ya kaiga ba iya shaida duk wanda ya mutu, saboda yanayin ƙonewar da suka yi a cewar masu aikin ceto.

A gabashin kasar da yaki ya daidaita, masu fafutuka sun ce akalla mutane 20 ne aka kashe a hare-haren da sojoji suka kai tun ranar Lahadi.

Yaki dai ya barke ne a tsakanin sojojin Sudan da Dakarun Ba da Agajin Gaggawa na RSF tun daga watan Afrilun 2023, inda ya kashe dubun-dubatar mutane tare da haifar da gudun hijira mafi girman da matsalolin jin kai a duniya.

A halin yanzu dai dakarun biyu na ci gaba da gwabza kazamin fada a jihar Al-Jazira ta tsakiyar kasar Sudan mai arzikin noma, wadda ke karkashin ikon dakarun soji tun karshen shekarar da ta gabata.

A ranar Lahadin da ta gabata, sojojin kasar suka sanar da cewa kwamandan RSF na Al-Jazira, Abu Aqla Kaykal, ya fita daga dakarun sa-kai na RSF, inda ya kai dakaru masu yawa domin su fafata yaki kafaɗa da kafaɗa tare da sojojin Sudan.

Wannan lamari da i ya kasance babban koma baya na farko ga dakarun daukin gaggawa na RSF.

Mai magana da yawun hafsan sojojin kasar Abdel Fattah Al-Burhan ya ce Kaykal da sauran wadanda suka sauya sheka sun samu afuwa domin samun natsuwa a cikin zukatansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)