Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a Misira ta yiwa Turkiyya godiya

Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a Misira ta yiwa Turkiyya godiya

Shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a Misira ya bayyana cewa suna yaba wa shugaba Recep Tayyip Erdogan, gwamnatin Turkiyya da kuma al'umman Turkiyya baki daya.

Mataimakin Shugaban Majalisar Ikhwan, Ibrahim Munir, a cikin wata rubutacciyar sanarwa ya ce Shugaban Kwamitin Kungiyoyin Masarawa, wadanda suka hada da wakilan kungiyoyin siyasar Masar ya bayyana cewa sun ziyarci Ankara babban birnin Turkiyya a ranar 21 ga watan Afirilu domin isar da bukatun ‘yan gudun hijira Masarawa dake Turkiyya da kuma sanin halin da suke ciki.

Munir, wanda ya saurari matsalolin da 'yan gudun hijirar Masar suka fuskanta wadanda suka sami aminci da tsaro a Turkiyya, ya nuna matukar godiyarsa ga dukkan cibiyoyi da kungiyoyin Turkiyya.

A cikin bayanin Munir ya kara da cewa,

"A matsayin mu na Ikhwan, muna da bashin godiya ga shugaban kasar Turkiyya, gwamnatin Turkiyya da kuma al'umman kasar baki daya, kuma a wannan mahallin, muna so mu kasance masu biyayya ga dokokin kasar Turkiyya da kuma kasancewa masu matukar godiya ga irin karamci da kara da al'umman Turkiyya suke nuna muna da ma ga Misirawan masu neman mafaka a kasarsu"


News Source:   ()