Kotun Tunisia ta ɗaure ƴan adawa tare da hana su takara

Kotun Tunisia ta ɗaure ƴan adawa tare da hana su takara

An yanke hukuncin ne a kan Abdel Latif Mekki, da Nizar Chaari, da Mourad Massoudi, sai kuma Adel Dou

Tuni dai ‘yan siyasa suka fara zargin an dauki  matakin da nufin kawar da manyan masu fafatawa da shugaba Kais Saied dake mulkar kasar a yanzu.

Hukuncin ya futo da  fargabar jam'iyyun adawa karara, hakan yasa 'yan takara, da kungiyoyin kare hakkin dam Adam suka zargi hukumomi da yin amfani da takunkumi da kuma tursasawa ba bisa ka'ida ba domin tabbatar da sake zaben shugaba maici a yazu a zaben da za’a gudanar na ranar 7 ga watan Oktoba.

Ahmed Nafatti, shugaban  yakin neman zaben na Mekki, ya ce har yanzu suna shirin mika takardar tsayawa takara a  Talatar nan.

Da yawa daga cikin shugabannin Jam’iyyun adawa  na daure a gidan yari, hakan tasa suka zargi gwamnatin Saied da matsin lamba kan bangaren shari’a don murkushe abokan hamayyarsa a zaben 2024 da kuma share masa hanya ta sake lashe zabe karo na biyu sai dai shugaban ya musanta hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)