
Bayanai sun ce baya ga guduwa daga fagen daga, Sojojin na Congo sun kuma aikata fyaɗe ga tarin mata tare da kisan fararen hula aƙalla 12 da kuma cin zarafin wasu dama kama daga azabtarwa da kuma ƙwace dukiyoyinsu.
A cewar wasu bayanai, sojojin sun riƙa shiga gidajen jama’a a ƙauyukan Kabare da Kalehe na gabashin lardin na kudancin Kivu tare da aikata musu cin zarafi.
Tun a jiya Litinin aka gurfanar da Sojojin gaban kotun ta Bukavu inda aka fara sauraren ƙarar kan tuhumar da ake musu, a wani yanayi ƴan farar hula ke neman zartas musu da hukuncin kisa.
Majiyoyi na nuna yiwuwar iya aiwatar da hukuncin na kisa matuƙar aka samesu da laifin da ake tuhumarsu musamman ganin yadda ƙasar ta dawo da aiwatar da hukuncin kisa cikin watan Maris, wanda ya janyo mata kakkausar suka daga masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam.
Rabon da Congo ta aiwatar da hukuncin kisa gabanin dawo da dokar a yanzu tun shekarar 2003.
Wani mazaunin garin Kavumu mai suna Zawadi Chapo Ombeni ya shaidawa zaman kotun cewa Sojoji sun ƙwace masa kuɗin dake hannunsa lokacin da ya ke shirin guduwa daga ƙauyen don kaucewa barazanar mayaƙan M23.
Daga farkon watan Janairun shekarar nan kawo yanzu alƙaluma na nuna cewa an kashe fararen hular da yawansu ka iya haura dubu 3 bayan da mayaƙan M23 masu samun goyon bayan Rwanda ke ci gaba da faɗaɗa mamayarsu a sassan ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI