Kotun ƙolin Mozambique ta tabbatar da nasarar jam'iyya mai mulki

Kotun ƙolin Mozambique ta tabbatar da nasarar jam'iyya mai mulki

Hukuncin da kotun ta yanke a yau litinin na tabbatar da nasarar shugaba Daniel Chapo, bayan zaɓen ƙasar da aka gudanar na ranar 9 ga watan oktoban shekarar 2024 mai ƙarewa, ya zo wa ɗimbin jama'ar ƙasar a wani yanayi na rashin gamsuwa da hakan, baya ga jam'iyyun adawa da ke iƙirarin jam'iyyar Frelimo ta yi maguɗi a zaɓen.

Kasancewar wannan kotu ita ce mataki na ƙarshe a shari'ar ƙasar , ya sanya al'umma ke kokawa game da daɗewar jam'iyyar frelimo a mulkin ƙasar kusan shekaru 50, tun daga shekarar 1975.

Bugu da kari, masu sanya ido kan zaɓen daga yammacin turai sun ƙi amincewa da sahihancin zaɓen yayin da ƙasar ta shiga rikice-rikice tun bayan sanar da sakamakon zaɓen a wancen lokaci.

Rahotanni sun bayyana cewar kimanin mutane 130 ne suka rasa rayukansu yayin artabu da ƴan sanda, sai dai ana hasashen rikici zai tsananta bayan hukuncin kotun kolin da ya tabbatar da Shugaba Daniel Chapo a matsayin zaɓabɓen shugaban ƙasar.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya sanar da cewa an samu koma baya a tattalin arziƙin Mozambique, sanadiyyar rikicin siyasa da ƙaƙƙarfar guguwar Chido da ta afkawa yankin, inda tuni aka tabbatar da mutuwar mutane 94.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)