Tuni dai aka shiga zaman ɗar-ɗar a sassan ƙasar ta Mozambique da ke kudancin Afrika musamman ganin irin asarar rayukan da aka tafka bayan sanar da sakamakon zaɓen tun a baya da ya haddasa ƙaƙƙarfar zanga-zanga.
Mozambique mai yawan jama’a miliyan 35 da ta samu ƴanci daga Afrika ta kudu, tun daga shekarar 1975 ta ke ƙarƙashin mulkin jam’iyyar ta Frelimo wadda a wannan karon ɓangarorin adawa suka sha alwashin kayar da ita amma kuma suka kasa, ko da ya ke sun yi zargin tafka maguɗi da ya baiwa ɗan takarar ta jam’iyya mai mulki Daniel Chapo nasara.
Masu sanya idanu na ƙasashen yammacin duniya sun ce ba a gudanar da zaɓen na Mozambique a bisa sahihanci ba, kuma an tauye ƴancin masu kaɗa ƙuri’a yayinda ƙumbiya ƙumbiya ta dabaibaye tsarin tafiyar da zaɓen wanda ya sanya shakkun tabbatuwar zarge-zargen na maguɗi.
A hukuncin da kotun ta yi zaman yankewa jiya Litinin ta tabbatar da cewa Daniel Chapo shi ne halastacce kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mozambique bayan gaza samun duk wata hujja da ke nuna ba shi ya lashe zaɓen ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI