Kotun Kundin Tsarin Mulki ta Jamhuriyar Kongo ta amince da Shugaban Kasar Denis Sassou Nguesso ya ci gaba da mulki.
Shugaban Kotun Kundin Tsarin Mulki Auguste Iloki ya shaida cewa, ya tabbatar da Nguesso a matsayin Shugaban Kasa sakamakon samun kusan kaso 88 na kuri'un da aka jefa a ranar 21 ga Maris.
Iloki ya shaida cewa, an duba dukkan korafe-korafen 'yan adawa, kuma an gano ba su da tushe balle makama a saboda haka aka yi watsi da su.
Kaso 67,55 na masu jefa kuri'a ne suka fita zabe inda aka sake zabar Nguesso a karo na 2 na shekaru 5.
Jami'an Tarayyar Afirka da suka sanya idanu a zaben na Kongo sun bayyana an samu 'yan matsaloli sakamakon katsewar yanar gizo a dukkan fadin kasar.
Nguesso mai shekaru 77 na daga cikin shugabannin Afirka da suka dade a kan mulki, kuma a ranar 24 ga Janairu ya baiyana zai sake tsayawa takarar Shugaban Kasa.
A shekarar 2016 aka zabe shi a matsayin Shugaban Kasa bayan ya samu kaso 60 na kuri'Un da aka jefa.
Tun shekarar 1997 Nguesso ya ke shugabantar Jamhuriyar Kongo, a tsakanin 1979-1992 ma ya shugabanci kasar.