Kotun kolin Masar ta amince da a zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane 6 da aka tuhuma da laifin kashe mutane 3 a tsakanin shekarun 2013 da 2015.
Kamfanin dillancin labarai na Masar ya bayyana cewar, kotun kolin kasar ta yi watsi da bukatar daukaka kara ta mutanen 6 inda ta kuma tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke musu.
Kotun ta kuma dauki matakin sassauta hukuncin daurin rai da rai da aka yankewa wasu mutanen su 25, zuwa daurin watanni 10 a gidan kurkuku.
A zaman kotun hukunta manyan laifuka ta Alkahira a shekarar 2019 ne aka yanke hukuncin kisa ga mutanen 6 bisa zargin su da kashe mutane 3 a tsakanin shekarun 2013-2015 da kuma kafa kungiyar ta'adda.