Kotun Kenya ta dakatar da maye gurbin tsohon mataimakin shugaban kasar da aka tsige

Matakin kotun na zuwa ne a wani lokaci da majalisar dokokin kasar ta amince da da nadin Kithure Kindiki da shugaban kasar William Ruto ya yi, sa'o'i kadan bayan amincewa da tsige Rigathi Gachagua.

Mataimakin shugaban Kenya da aka tsige, Rigathi Gachagua. Mataimakin shugaban Kenya da aka tsige, Rigathi Gachagua. AP - Andrew Kasuku

Kotun ta bayar umarnin dakatar da wannan mataki har zuwa 24 ga Oktoba,kamar dai yada Alkalin kotun Chacha Mwita ya yi la'akari da cewa karar da Rigathi Gachagua ya shigar,za su mayar da hankali a kai domin duba abinda doka ta yi tanadi a kai.

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda aka kwantar da shi a asibiti sa’o’i kadan kafin zaben ‘yan majalisar dattijai na ranar alhamis Alhamis, ya kalubalanci maye gurbinsa a gaban kotu, inda ya bayyana hakan a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar ta Kenya.

Shugaban kasar Kenya William Ruto Shugaban kasar Kenya William Ruto © Thomas Mukoya / REUTERS

Masu lura da siyasar kasar ta Kenya na bayyana cewa,babu shaka da sauren aiki a gaban shugaban kasar da zai fuskanci adawa daga tsohon mataimakin sa har idan aka tabbatar da tsige.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)