Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ta yanke hukuncin daurin shekaru 25 ga daya daga cikin Kwamandojin Kungiyar gGwagwarmayar Ubangiji ta 'yan waren Uganda Dominic Ongwen sakamakon samun da aikata laifukan yaki.
A zaman shari'ar da Ongwen ya halarta a birnin Lahey na kasar Holan, an same shi da hannu a aikata laifuka 61 na yaki da keta hakkokin dan adam.
Da yake karanta hukuncin, shugaban alkalan kotun Bertram Schmitt ya ce, sakamakon nadama da Ongwen ya yi, an rage hukuncin daga na daurin rai da rai zuwa na shekaru 25 a gidan maza.
tare da wannan hukunci, sau 6a ana yankewa Ongwen hukunci kan keta hakkokin dan adam.
A zaman da kotun ta yi a ranar 4 ga fabrairu ta samu Dominic Ongwen da laifin aikata laifukan yaki da keta hakkokin dan adam kan fararen hula da suka gudu daga rikicin Uganda zuwa sansanonin Pajule, Odek, Abok da Lukodi.
Ongwen ya bayar da umarni an kai hare-hare kan sansanonin da fararen hula suke zaune, kuma shi aka dorawa alhakin laifukan da mayakan Dakarun gwagwarmayar Ubangiji suka aikata.
An samu Ongwen da lafukan da suka hada da; kisa, zalunci, bautar da mutane, sace dukiyoyi, fyade, yi wa mata ciki ta karfi da yaji da bawa yara kanana makamai.