Kotun Benin ta zartas da hukuncin dauri ga wasu tsoffin mukarraban Patrice Talon

Kotun Benin ta zartas da hukuncin dauri ga wasu tsoffin mukarraban Patrice Talon

Kusan kwana daya bayan da kotun ta zartas da hukunci dauri na shekaru 20 ga wasu daga cikin tsofin aminan shugaban kasar Patrice Talon ,da suka hada da babban aminin sa Olivier Boco da tsohon Ministan wasannin kasar,ra’ayoyi sun babbanta dangane da wannan hukunci da wannan kotu da aka sani da Criet ta zartas.

Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon AFP - RAFAELA ARAUJO

Dan kasuwa Olivier Boko da tsohon ministan wasanni Oswald Homeky an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20, da diyya da kudin ruwa CFA biliyan 60 da kuma tarar CFA biliyan 4.5.

Wani abin lura a wannan zaman kotu,mutanen da ake tuhuma ba su wakilcin lauya ba, Olivier Boko, surukinsa Rock Nieri,da kuma Oswald Homeky duk an yanke musu hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari na CFA biliyan 4.5 da kuma jimillar CFA biliyan 60 na diyya.

Bisa shawarar mai gabatar da kara, ta yi la'akari da cewa kudaden da aka gano a gidan tsohon ministan wasanni a lokacin da aka kama shi, Olivier Boko da surukinsa sun yi amfani da su wajen siyan shugaban masu gadin fadar shugaban kasa kuma ' Oswald Homeky ya yi aiki a madadin dan kasuwan, mutum daya tilo da zai iya tara irin wannan kudi.

 Boni Richard Ourou dan siyasa kuma shugaban MLB a kasar ta Benin,bayan bayyana cewa Shugaban kasar a wannan lokaci ya na mai fuskantar wani mawuyacin hali,kasancewa ya rasa babban abokinsa da kotu ta zartaswa hukunci dauri, Richard Boni ya bayyana cewa,wannan al’amari za ya sa shugaban kasar  ya yi tunani a kan yanayin dangantakarsa da mutanen da suke aiki  da shi.

Richard Bonou Orou Richard Bonou Orou © media

Richard Boni Ourou ya yi nazari kan cewa burin waɗanda ke kewaye da mu wani lokaci yana iya ɓoye nufin farko kuma ya kai ga zaɓin nadama.

Yana da muhimmanci cewa, a lokuta masu zuwa, shugaban kasa ya kula da kansa da kuma mulkin da yake gudanarwa. Bari wannan wahalar ta zama wata dama ta zurfafa tunani a kan dangantakar da yake da shi da kuma yadda yake zabar abokan aikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)