Kotun Afirka ta Kudu ta ba da umarni ga 'yan sanda na su kawo karshen killace masu hakar ma'adinai

Kotun Afirka ta Kudu ta ba da umarni ga 'yan sanda na su kawo karshen killace masu hakar ma'adinai

'Yan sanda da motocin daukar marasa lafiya sun kasance a wurin, a Stilfontein, wurin da ke da nisan kilomita 140 kudu maso yammacin Johannesburg.

‘Yan sanda sun kira kwararru a yau Asabar don tantance wuraren da masu aikin suka buya a cikin ramen,kamar yadda kakakin ‘yan sandan Athlenda Mathe ya shaida wa manema labarai.

Sai yan lokuta da sanar da haka ne umarnin kotu ya kawar da wannan zabin na ‘yan sanda.

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa da mataimakin sa Paul Mashatile Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa da mataimakin sa Paul Mashatile © Nic Bothma / Reuters

 

Umurnin kotun Pretoria ya ce:matakin da zai biyo baya ,shina na kulle ma’adinan na Stilfontein,kotu ta karasa da cewa,babu wanda zai ci gaba da aiki a wannan wuri ,kama daga  bangren gwamnati ko masu zaman kan su.

Alkalin ya kara da cewa "Duk masu hakar ma'adinai da suka makale a cikin ma'adinan za a ba su izinin fita; baya gare su,babu wani ma'aikacin da zai iya shiga cikin ma'adinan nan gaba.

A farkon wannan makon, wani dan yankin ya yi ikirarin cewa an gaya masa cewa akwai masu hakar ma'adinai kusan 4,000 a karkashin kasa.

‘Yan sandan da ke magana a farkon makon nan, sun ce adadin ya kai daruruwa, amma masu hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba sun fuskanci kame idan sun fito fili.

Ranar Alhamis aka fito da gawa daga mahakar. Rundunar ‘yan sandan ta kuma katse kayan abinci da ruwan sha ga masu hakar ma’adinan karkashin kasa.

A ranar Laraba, minista a fadar shugaban kasar Khumbudzo Ntshavheni ya shaidawa manema labarai cewa gwamnati ba ta da niyyar shiga cikin lamarin.

Dubban masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, yawancinsu sun fito daga wasu kasashe, an ce suna gudanar da ayyukan hakar ma'adinai da aka yi watsi da su a Afirka ta Kudu mai arzikin ma'adinai. Waɗanda aka fi sani da "zama zamas".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)