Kotu tayi watsi da bukatar mataimakin shugaban Kenya kan yunkurin tsige shi

Kotu tayi watsi da bukatar mataimakin shugaban Kenya kan yunkurin tsige shi

Lokacin da yake yanke wannan hukunci a jiya talata, alƙalin babbar kotun mai shari’a Enock Chacha Mwita, ya ce ta la’akari da abubuwan da ke ƙunsh a kundin tsarin mulki, majalisar dokoki tana da damar gudanar da bincike kan duk wani zargi da ake yi wa mataimakin shugaban ƙasa, saboda haka yunƙuri domin hana wannan bincike zai kasance iya kasancewa karen-tsaye ga dokokin ƙasar.

To sai dai duk da cewa bai kasance a cikin zauren shari’ar ba, amma lauyen da ke kare mataimakin shugaban ƙasar ya ce za su ɗaukaka don nuna rashin gamsuwa a game da wannan hukunci.

Tun a cikin makon jiya ne ƙaramar majalisar dokokin Kenya ta kaɗa ƙuri’ar tsige Mista Gachagua mai shekaru 59 a duniya, saboda a cewarta ta same shi da laifin ƙin yi wa shugaban ƙasa William Ruto biyayya sannan kuma ya handame dukiyar al’umma.

Kamar dai yadda yake rubuce a cikin kundin tsarin mulki, ana buƙatar ƙuri’u 45 daga cikin 68 da ake da su a cikin majalisar dattawa ne domin tsige mataimakin shugaban, kuma idan hakan ya tabbata, Rigathi Gachagua zai kasance mataimakin shugaban ƙasar Kenya na farko da aka tuɓe daga mukaminsa a tarihin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)