Kotun dai ta kama Thomas Kwoyelo wanda ya rikiɗe daga soja zuwa ɗan tawaye da laifukan kisan kai, fyaɗe, satar kayayyakin jama’a da kuma bautar da bi’adama.
A watan Agustan da ya gabata an kama Kwoyelo da laifuka 44 cikin 78 da ake tuhumarsa da aikatawa, kuma mafi yawansu ya aikata su ne a yaƙin da ya faru tsakanin shekarun 1992 zuwa 2005 da ya faru a ƙasar.
Dukannin alƙalan kotun da suka saurari shari’ar sun amince da hukuncin da aka yanke masa, sai dai kuma an bashi damar ɗaukaka ƙara.
An dai fara shari’ar Kwoyelo a shekarar 2019, kuma tun 2009 yake tsare a gidan yari, yayin da mahukunta ke ƙoƙarin gano hanyoyin da za’a bi wajen yi masa shari’a ba tare da cikas ba.
A bayanin da ta yi bayan kammala shari’ar ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Human Rights Watch ta ce wannan wata dama ce ta musamman da iyalan waɗanda ibtila’in ya shafa su sami adalci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI