Alkalin kotun mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni a zaman kotun da ya gudana.
Jam’iyyun APP, ADP da kuma SDP ne dai suka shigar da ƙarar hukumar ta KANSIEC kan abinda suka kira aringizo a kuɗaɗen sayen fam din don hana ƴan takarar ƙananan jam’iyyu shiga zaɓen.
Bayan umarnin da alƙalin ya bayar na dakatar da sayar da fam ɗin kan wannan adadin kuɗi, ya kuma ɗage ci gaba da sauraren shari’ar har zuwa ranar 15 ga watan da muke ciki na Satumba.
Ƙananan jam’iyyu a jihar na ganin cewa hukumar ta sanya adadin kuɗin ne kawai don hana ƴan takarar su shiga zaɓen da kuma amfani da hakan wajen musguna musu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI