Bayanai sun ce an kama Abir Moussi mai shekaru 49 tun a shekarar da ta gabata, bayan da ta chachaki tsarin tafiyar da hukumar zaɓe ta ƙasar da kuma dokokin da suke riƙe da ita.
Kotun ta kama Abir da laifin yiwa tsarin dokokin ƙasa zagon ƙasa da kuma yaɗa labaran ƙarya da kuma cin zarafin gwamnati.
To sai dai kuma lauyan ta Nafaa Laribi ya ce wannan ba komai bane illa wani yunkurin hanata shiga zabe da kuma razanar da sauran abokan adawa.
Labiri ya kuma ce wannan hukunci bai ragewa Moussi kwarin gwiwar sauya akalar gwamnatin ƙasar zuwa kan ingantacciyar dimokradiyya ba, kuma tuni suka kammala duk wasu shirye-shirye na daukaka ƙara.
Wannan hukunci dai ya ƙara rura wutar siyasa a ƙasar wadda ke fama da matsalolin tattalin arziki da tsadar rayuwa, yayinda ƴan ƙasar ke kokawa da manufofin gwamnatin Kais Saeed.
Idan har ta tabbata Moussi ta bi ƙarin jiga-jigan ƴan siyasa da ke ƙasar zuwa gidan yari, Kais Saeed bashi da wata gagarumar matsalar adawa a zaɓen da ke tunkarar ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI