Kotu ta amince da Assimi Goita a matsayin shugaban kasar Mali

Kotu ta amince da Assimi Goita a matsayin shugaban kasar Mali

Kotun tsarin mulkin Mali ta amince da shugabancin Kanar Assimi Goita, mutumin da ya jagoranci juyin mulkin a ranar 24 ga watan Mayu.

A cikin bayaninta, Kotun Kundin Tsarin Mulki ta sanar da cewa Assimi Goita ya samu amincewar ta na zama shugaban kasar.

Goita ya bayar da umarnin tsare wasu manyan jami'ai, ciki har da shugaban majalisar rikon kwarya Bah Ndaw da firaiminista  Moctar Ouane, yana mai cewa ba a yi daidai a garambawul da aka yi wa majlisar ministocin kasar a ranar 24 ga Mayu ba.

An saki Shugaban Majalisar rikon kwarya Bah Ndaw da Firayim Minista Moctar Ouane a jiya bayan da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta tura wakili zuwa kasar don sasantawa.


News Source:   ()