Kotu a Jamhuriya Nijar ta aike da Moussa Tchangari zuwa gidan yarin Filingue

Kotu a Jamhuriya Nijar ta aike da Moussa Tchangari zuwa gidan yarin Filingue

A watan Disamba shekara ta gabata wasu mutane dauke da makamai su kayi dirar mikiya a gidansa tareda yin awon gaba dashi bayan sun  kwace na’urarsa da wayoyin hanu da kuma jakarsa ta balaguro.

Bayan shafe sama da wata guda yana  a offishin jami’an yaki da ta’addanci,  a rana  juma’a Moussa Tchangari ya gurfana a gaban alkali domin sauraron zarge-zargen da ake yi masa.

Tchangari ya  bayyana a gaban kotun da harabarta  aka jibge dimbin jami’an tsaro, tareda rakiyar lauyoyi da danginsa da kuma sauran abokan gwagwarmaya kare hakin bil adama.

Kotu na tuhuma Moussa Tchangari da laifukan da suka shafi cin amanar kasa, hada baki da muyagu da kuma goyan bayan aikata ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)