Kotu a Faransa na zargin ƙusohin gwamnati da naɗe hannu lokacin kisan ƙare dangin Rwanda

Kotu a Faransa na zargin ƙusohin gwamnati da naɗe hannu lokacin kisan ƙare dangin Rwanda

Kotun ta fara sauraron ƙorafin da ƙungiyoyin waɗanda suka tsira domin bincikar irin rawar da Faransa ta taka a wancan lokacin.

Masu shigar da ƙara na fatan za biyasu diyyar da suka nema, bayan sun zargi Faransa da yin shiru lokacin da ake taimakawa bangarorin da ke rikici da juna da makamai da kuma watsi da halin da fararen hula ke ciki.

Waɗanda suka tsira a wancan lokacin dai sun nemi a biya su diyyar dala miliyan 540.

An sha zargin ƙusoshin na wancan lokaci da goyon bayan gwamnatin da ke kan karagar mulki a lokacin da aka shafe kwanaki 100 ana kashe-kashen da masu tsattsauran ra'ayin Hutu suka yi.

Yayin da shari’ar da aka yi a baya ba ta yi nasara ba, wannan shi ne karon farko da kotun gudanarwa ke sauraren ƙarar.

Fiye da mutane miliyan guda aka kashe a tashin hankalin da ya kawo ƙarshe a lokacin da ƴan tawayen ƙungiyar kishin ƙasar Rwanda ƙarƙashin jagorancin shugaba Paul Kagame suka kori sojojin Hutu da miliyoyin fararen hula.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a baya ya ce ya yi imanin Faransa da ƙawayenta za su iya dakatar da kisan kiyashin, amma suka gaza aiwatarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)