A cikin awanni 24 Koroya ta yi ajalin mutum 712 a kasar Afrika ta Kudu lamarin da ya kara yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar a kasar karuwa zuwa dubu 35,852 a jumlace.
Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Zweli Mkhize ya bayyana cewa a yankin gundumar KwaZulu-Natal aka fi samun yawan mace-mace sanadiyar cutar inda mutum 232 suka rasu.
Gundumar dake binta baya kuwa ita ce ta Yammacin Cape da mutum 162 sai gundumar Gauteng da suka hada da yankin Pretoria inda aka samu rashin rayuka 114.
Haka kuma a gabashin Cape inda aka rasa rayuka 97 a sauran gundumomin kuma a ko wa ce akwai akallan rashin rayuka 60 a cikin awannin 24.
Mkhize ya kara da cewa kasar ta sake samun yawan mutum dubu 18,503 dauke da cutar bayan gudanar da gwaji ga mutane dubu 74,830 a cikin awanni 24.