An bayyana cewa karo na ukun sabon nau'in kwayar cutar coronavirus (Kovid-19) ya fara a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Ministan Kiwon Lafiyar kasar Jean Jacques Mbungani ya bayyana a cikin rubutaccen bayanin nasa ya na cewa, an sami gagarumar karuwar kamuwa da cutar Kovid-19 a cikin kasar a cikin makwanni 4 da suka gabata, kuma an fara daukar matakai akan annobar karu na ukuç
Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a kasar ya kuma ja hankali kan karuwar masu kamuwa da cutar a kasar inda aka gano kwayar cutar ta Indiya da Afirka ta Kudu, 'yan sa'o'i kadan kafin sanarwar Mbungani.
A kasar, wanda ke da yawan mutane kusan miliyan 86, yawan masu kamuwa da cutar ya rubanya ninki biyu a watan da ya gabata.