Babbar Kotun Uganda ta umarci gwamnatin kasar da ta tsara kudaden da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ke karba don kula da marasa lafiyar dake fama da COVID-19.
Bayan zagaye na biyu na COVID-19, an zargi cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu da yawa da cin riba daga cutar, suna karɓar kuɗaɗen da suka wuce kima.
A wasu takardun rasit da wasu iyalan wadanda suka kamu da cutar Korona suka yada, anga cewa sun kashe fiye da dala dubu 15,000 akan mutun daya da ya yi fama da cutar a asibitoci masu zaman kansu, wannan ya wuce kima musanman a kasar Uganda inda kimanin kudin shigar mutun daya a shekara yake dala dubu 777.
Wasu cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu har ma sun ki sakin gawarwakin marasa lafiyar da suka kamu da cutar har sai an biya kudin maganin da aka bari a baya, yayin da wasu ke neman jingina kamar littattafan mota da lakabin mallakar fili kafin su kula da marasa lafiyar COVID-19.