An sake kai wani hari a wata makarantar kwana tare da sace dalibai da dama a jihar Kaduna dake kasar Najeriya.
Shugaban 'yan sandan jihar Kaduna Samuel Aruwan, ne ya bayyana cewa an kai harin ne a makarantar gandun dajin dake yankin Mando.
Aruwan, ya bayyana cewa an sace dalibai da dama an bai bayyana iya yawan da aka sacen ba.
Ya tabbatar da cewa an baza jami'an tsaro a yankin.
Da yawan al'umma arewacin Najeriya na cikin zullumi tun bayan da 'yan bindiga suka fara kai hare-hare a makarantu suna sace yara.
Wasu masanan kasar kuwa na tambaya da yin sharhi ne akan yadda za'a magance matsalar da kuma ko yaushe ne matsalar za a iya shawo kanta.