An sanar da cewa Hukumar Leken Asirin kasar Amurka wato CIA na cigaba da fadada sansanin sararin samaniyar da ta kafa a shekarar 2018 a kasar Nijer.
Kamar yadda Jaridar New York Times ta rawaito kamar yadda sabon tauraron dan adam ya dauko sansanin sararin samaniyar da Amurka ta kafa a shekarar 2018 a daidai garin Dirkou dake kasar Nijer ya fadada kwarai da gaske.
An tabbatar da cewa an kara tsayin sansanin lamarin da zai kara sanya samar da tsaro a yankin. An dai yi amfani da jirgi mara matuki kirar MQ-9 Reaper da zummar inganta sansanin.
Hukumar CIA ta kafa wannan sansanin da niyar kara samar da tsaro da kauda aika-aikan kungiyoyin Al-Kaida, DEASH da wasu makamantansu a yankin zuwa kudu maso yammacin Libiya bayan harin da aka kai a watan Oktoban 2017 da ya yi sanadiyar rayukan sojojin Amurka 4.
A gefe guda kuma, a yayinda mai magana da yawun Hukumar CIA Timothy L. Barrett ya ki cewa uffan akan lamarin, mai magana da rundunar sojojin Amurka a Nijer Nicole Kirschmann ya bayyana cewa sansanin ba na dindindin bane sai dai bai bayar da bayani game da fadada sansanin da aka yi ba.