Binciken da aka gudanar akan ‘yan fafutuka da masu rajin kare hakkin bil adama cikin kasashe shida a Afirka wadanda suka hada da Nijar,Benin, Gabon, Kamaru, Cote d’Ivoire da Chadi ya bayyana karara tareda gamsassun hujjoji yadda al’umomin wadanda kasashen suka yi watsi da salon siyasa Fransa akan nahiya Afirka .
Yawancin wadanda binciken ya bi takansu sun shaida cewa al’umma a Afirka na nuna kyama ne kan salon siyasa Faransa ga kasashen Afirka bawai ga Faransawa su kansu ba, suna masu kafa hujja da cewa babu Bafaranshe daya da aka kaiwa hari a Afirka da sunan nuna kyamar.
Ba kamar yadda akayi zato ba, wadanda suka gudanar da bincike sun ce yada labaran karya kan manufofin Faransa a nahiya Afirka da ake zargin Rasha da ‘yan barantada yi bai yiwani tasiri wajan sauya tunanin ‘yan Afirka gameda salon siyasar Faransa ba.
Kazalika binciken ya bankado yadda janye runduna sojojin Barkhane daga yankin Sahel ya zubar da mutuncin Faransa a idon Afirka.
Sai dai masu binciken sun nuna cewa jiji da kai da rashin kwatanta adalci tsakanin kasashe na shugaban Faransa Emmanuel Macron na daga cikin abubuwan da suka ruwa wuta kyamar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI