A Habasha, wasu kungiyoyi dauke da makamai sun kashe fararen hula da dama a harin da suka kai a wani kauye.
Fararen hula da dama sun mutu a harin da wasu kungiyoyi dauke da makamai suka kai a wani kauye a jihar Benishangul Gumuz da ke yammacin kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Amhara (AMMA) ya rawaito cewa kwana daya bayan ziyarar Firaminista Abiy Ahmed, maharan sun kİ hari kan wani kauye a yankin Metekel na lardin inda suka kashe mutane da dama.
Shaidun gani da ido na yankin sun bayyana cewar maharan wadanda har yanzu ba a gano ko su waye ba, sun bude wuta a kauyen kuma suka cinna wa gidaje wuta.
Wasu kafofin labarai na cikin gida sun bayyana cewar wadanda suka mutu sun haura 90.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed ya yi alkawarin "kawo karshen rikice-rikicen kabilanci da tashe-tashen hankula a yankin" a yayin ziyarar da ya kai garin Metekel.