Ƙungiyar M23 da ke samun goyon bayan Rwanda, a makonnin baya-bayan nan ta kwace wasu manyan biranen ƙasar guda biyu a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, lamarin da ya bai wa kungiyar ta ƴan tawaye damar zama a yankin tun bayan sake ɗaukar makamai a ƙarshen shekarar 2021.
A yayin da ya isa Kinshasa, babban birnin kasar, Khan ya shaida wa manema labarai cewa suna cikin matukar damuwa da abubuwan da ke faruwa a Congo a baya-bayan nan.
Khan ya ƙara da cewa ya zama wajibi waɗanda ke yaƙi da juna su bi dokokin jin-ƙai na ƙasa da ƙasa domin kulawa da haƙƙoƙin mata da ƙananan yara da kuma kauce wa kisan gilla.
Sannan kwararru na Majalisar Ɗinkin Duniya suka ce ƙungiyar ta M23 na samun goyon bayan sojojin Rwanda kusan 4,000 ne a ɗauki-ba-daɗin da suke yi da sojojin ƙasar ta Congo.
Tun bayan sake ɓullar ƙungiyar ta M23, fada tsakaninta da sojojin Congo ya haifar da matsalar jin-ƙai a yankin da ke fama da rikici tsawon shekaru 30.
Khan ya ce wannan lokaci ne da za su gani ko dokokin jin-ƙai na ƙasa da ƙasa za su iya yin tasiri a wannan lokaci da al’umar ƙasar ke da matukar buƙatar ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI