Kenya za ta sayi motocin soji masu sulke daga Turkiyya

Kenya za ta sayi motocin soji masu sulke daga Turkiyya

Rundunar Sojin Kenyaza ta sayi motocin soji masu sulke guda 118 daga wajen Turkiyya.

Kakakin Rundunar Sojin Kenya Zipporah Kioko ya shaida cewa, a aiyukan da suke yi na yaki da 'yan ta'addar Al-Shabab da kare iyakokin kasar, za su sayi motoci masu sulke guda 118 daga kamfanunnukan samar da kayan tsaro na Turkiyya.

Kioko ya jaddada cewar wadannn motoci masu sulke da ke daukar sojoji, za su bayar da damar samar kariya ga dakarun Kenya, kuma an kusa kawo karshen cimma yarjejeniyar sayen motocin guda 118.

Motar sojoji da ake wa lakabi da sunan Hizir, ita ce mafi karfin inji da nagarta a Turkiyya, kuma tana da jan hankali kan yadda ta ke da juriya a filin yaki.

Motar Hizir na da ikon bijirewa fashewar bam da harbo makaman roka, kuma tana ja da gaba da baya, sannan kuma tana da karfin dawaki 400.

Motar ta cika ka'idojin motocin soji na Kawancen NATO.


News Source:   ()