Hukumomi a kasar Kenya sun fara gudanar da bincike akan labarin da ya zama ruwan dare na satar kananan yara a fadin kasar.
Sufeto Janar na ‘yan sandar kasar Hillary Mutyambai ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike mai girma bayan rahoton BBC dake nuna cewa ana yawan sace-sacen yara daga asibitoci da titunan dake babban birnin kasar Nairobi.
Mutyambai, ya kara da cewa hukumar za ta yi aiki da haddin gwiwar kungiyoyi domin gudanar da bincike a asibitoci masu zaman kansu dama na gwamnati a kasar.
Mutyambai ya tabbatar da cewa bayan fara binciken an kame ma'aikatar lafiya uku, akan zarginsu da hada baki wajen satar yaran inda ya kara da cewa za a kuma kama wasu da dama.
Rahoton da kafar yada labaran BBC ta rawaito ya nuna cewa yara da jinjiran da ake sacewa daga asibitoci da titunan Nairobi ana siyar da mata kimanin dala 400 maza kuma kimanin dala 700.