Gwamnatin Kenya ta baiwa Majalisar Dinkin Duniya wa'adin makonni 2 na ta rufe sansanonin 'yan gudun hijira na Dadaab da Kakuma tare da mayar da Somaliyawa zuwa kasarsu.
Sakataren Majalisar Harkokin Cikin Gida ta Kenya Fred Matiang ya shaida cewa, sun dauki matakin rufe sansanonin Dadaab da Kakuma mafiya girma saboda barazanar tsaro da suke yi wa kasarsu.
Mitiang ya ce, sun aike da wasika da Kwamishiniyar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da 'Yan Gudun Hijira a Kenya Fadhilaa Addala inda suka ba ta makonni 2 da ta kwashe 'yan gudun hijirar Somaliya daga sansanonin.
Gwamnatin Kenya ta bayyana cewa, sansanonin na zama maboyar 'yan ta'addar Al-Shabab a saboda haka suka dauki matakin rufe su.
Kungiyoyin kare hakkokin dan adam da Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci Kenya da ta sake duba wannan mataki da ta dauka.