Kenya na shirn ɓullo da wani sabon haraji

Kenya na shirn ɓullo da wani sabon haraji

Ministan ƙudin Kenya John Mbadi ya sanar da sabon shirin yayin hira da wani gidan talabijin na ƙasar da aka watsa a daren Lahadi, inda ya ce matakin ba wai maido da ɗaukacin haraje-harajen da ya shafi al’umma bane baki ɗaya, dole za’a cire wasu daga cikin matakan da suka haifar da ce-ce-ku-ce a baya.

Shugaba ƙasar William Ruto ya yi gargadi game da gibin ƙudade da aka samu bayan da ya yanke shawarar janye ƙarin harajin da ya yi a watan Yunin da ya gabata, sakamakon mummunar zanga-zanagr da ta janyo asarar rayuka a birnin Nairobi.

Mista Mbadi ya ce gwamnati na duba yiwuwar ƙarin haraji a bangarori daban-daban har 49 a wani kokari na tara kusan shilling biliyan 150, kwatan-kwacin dalar Amurka biliyan 1 da dubu 200.

A cewar ministan sabon harajin zai shafi kayayyakin lantarki da kuma robobi, wanda gwamnati ta ce wani ƙoƙari ne na rage sharar robobi a ƙasar.

"Idan kuna cutar da muhalli to dole ne ku biya ƙudi, don taimakawa wajen gyara ɓarnar da kuka yi,"

Mbadi na ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴan adawar Kenya hudu da suka shiga majalisar ministocin da aka yi wa kwaskwarima bayan da Ruto ya sha alwashin samar da gwamnatin haɗin kan ƙasa mai fa'ida don kokarin magance matsalolin masu zanga-zangar, karkashin jagorancin matasa Gen-Z na Kenya.

Bayan soke dokar kudi ta 2024, da zai tara kusan dala biliyan 2.7 na haraji, Ruto ya sanar da rage kashe kudade da gwamnati ke yi tare da kara neman rance don toshe gibin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)