Yaro 1 ya mutu, wasu 3 sun jikkata sakamakon fashewar wasu kayan aiyukan soji a Libiya.
Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Farko da ke karkashin Ma'aikatar Lafiya ta Libiya, Usama Ali ya shaida cewa, wasu abubuwa sun fashe a yankin Ayn Zara da ke kudancin Tarabulus Babban Birnin Kasar.
Ali ya fadi cewa, fashewar ta afku a lokacin da wani yaro karami ya ke taba abun fashewar, kuma ya mutu yayin da wasu yara 3 suka jikkata.
Wadanda suka jikkata na cikin halin rai mutu kwakwai.
Ba a bayar da bayanan wadanne irin kayan aikin soji ne suka fashe ba.
A ranar 22 ga Mayu rundunar sojin Libiya ta sanar da cewa bayan an fatattaki mayakan Haftar daga kudancin Tarabulus, sun binne bama-bamai a yankunan Salahaddin, Al-Mashru'u da Ayn Zara.