Katsewa wutan lantarki ya jefa manyan biranen Kamaru cikin duhu

Katsewa wutan lantarki ya jefa manyan biranen Kamaru cikin duhu

Gariruwan da lamarin ya shafa sun hada da Yaounde,Douala, da Bafoussam.

Sai kuma yankunan Bamenda da Buea dukanin su a yankin masu amfani da turanci Ingilishi.

Da farko lamarin ya jefa jama’a kasar cikin dimuwa kahin daga bisani gwamnatin ta bakin ministan kula da albarkacin ruwa da makashi ya  kwantarda hankulan jama’a ta hanyar wata sanarwa da ya fitar.

A Douala kamar sauran biranen kasar, lamarin ya haifar da rudani da ce-ce kuce a shafukan sada zumunta har ya kai jama’a sun fara danganta batun da matsala tsaro.

Wata majiya ta kusa da gwamnati ta kwarmata cewa, katsewar wutan lantarkin ya haddasa tsoro a zukatan wasu manyan mutane saboda yanayin siyasar da aka shiga a kasar.

Sanarwa da gwamnati ta fitar, ta ce matsalar nada nasaba da lalacewar layin wutan lantarki dake samar da wuta ga jihohi 6 daga cikin 10 da kasar ta kunsa  abunda ya haifar raguwa karfin wutar.

Bayan gyaruwa al’amurra an bukaci jama’a da ka da suyi amfani da kayakin su na wuta har sai lokacin da wutar ta daidai ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)