Sakamakon karancin ruwan sama, kaso 70 na jama'ar Somaliya ba sa samun tsaftataccen ruwan sha.
Wakilin Kungiyar Farar Hula ta Kasa da Kasa ta Save the Children a Somaliya Muhammad Hasan ya fitar da rahoton biinciken da suka gudanar a yankuna 18 sakamakon zagayowar Ranar Ruwa ta Duniya.
Hasan ya shaida cewa, mutane da dama a Somaliya na fuskantar matsaloli saboda karancin ruwan sha.
Ya ce, "Sakamakon sauyin yanayi, kaso 70 na iyalai ba sa samun tsaftataccen ruwan sha."
Jami'in ya yi gargadi da cewa, kamar yadda aka gani a kasashe irin su Uganda, Kenya da Itopiya, matsalar ruwan na iya janyo rikicin samun abinci a Somaliya.