An bayyana cewa, kaso 10 cikin dari kacal na allurar riga-kafin Corona (Covid-19) da ake bukata a Afirka aka iya kaiwa nahiyar.
Daraktar Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) a Afirka Matshido Moeti a yayiin taron manema labarai mako-mako ta shaida cewa, a lokacin da ake bukatar allurar riga-kafin Corona miliyan 820 a nahiyar, kwaya miliyan 82 kawai aka iya kaiwa.
Ta ce, "A karshe akwai haske game da samar da allurar riga-kafin Corona ga Afirka, bai kamata a dusashe wannan hasken ba."
Moeti ta kara da cewa, an yiwa kaso 2 na al'umar nahiyar Afirka su biliyan 1,3 allurar riga-kafin Corona, kuma suna da damuwa matuka idan har aka gaza samun isasshiyar allurar riga-kafin.
Mutane dubu 167,599 cutar Corona ta kashe a Afirka, ta kuma kama jimillar mutane miliyan 6 da dubu 642.
Afirka ta Kudu, Morokko, Masar, Itopiya da Libiya ne suka fi samun wadanda suka kamu da cutar a Afirka.