Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, ya bayyana cewa Sassan da zasu sanya hadin gwiwa a tsakanin Aljeriya da Nijar na da matukar fadi, wanda ya yi kira da a kara karfafa mu’amala tsakanin kasashen biyu dake makwaftaka da juna.
A yayin bude taron, Zein ya kara da cewa hakan ya haifar da gudanar da wannan babban taron hadin gwiwar tsakaninsu, saboda akwai hanyoyi da dama da zasu amfana da ita.
Ya ci gaba da cewa, "Algeria da Nijar na da kwarin guiwar karfafa mu’amala tare da ba da gudummawar wannan hadin gwiwa, domin gudanar da wannan taro zai bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu wadda hakan zai ba da gudunmawa a kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro da ci gaban tattalin arziki.
A latsa alamar sauti domin sauraren bayanin:
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI