Macron ya bayyana haka ne, yayin jawabin buɗe taron Jakadun Faransa da yake jagoranta don sake nazari kan manufofinsu a ƙasashen ƙetare.
Chadi ce ta fara mayar martani kan kalaman shugaba Macron, ta cikin wata sanarwa da ministan harkokin diflomasiyyar kasar Abdurahmane Koulamallah ya karanto ta gidan talabjin din gwamnati.
Bayan bayyana damuwa kan kalaman da ya kira da na tozarci ga Afirka da ‘al’ummar ta, Koulamallah ya yi kira ga shugabanin Faransa da su mutunta ‘yan Afirka wadanda a cewarsa sukayi ruwa da tsaki wajan ceto Faransa daga rugujewa a yakin duniya na daya dana biyu ba tare da Faransa ta nuna godiyarta akai ba har yanzu.
Shima ministan kula da harkar manyan gine-gine Aziz Mahamat kuma mamba a kwamitin kwashe dakarun Faransa a kasar ya nemi Faransa ta darajarta zabin al’ummar Chadi
A nasa bangaren kuwa, Firaministan Senegal Ousmane Sonko wanda kasarsa a baya-bayan nan ta bukaci Faransa ta janye dakarunta daga kasar a wanan shekara ta 2025, ya musanta kalaman Macron inda ya ce an gudanar da tattaunawa gabanin fidda sanarwar janyewar dakarun Faransa a kasar, ya na mai cewa mataki ne da Senegal ta dauka a karan kanta a matsayin ta na kasa mai cikakken ‘yanci a wani sako da ya rubuta a shafinsa na X.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI