Karancin abinci na kashe yara kanana a Najeriya

Karancin abinci na kashe yara kanana a Najeriya

Yara kanana 81 ne suka rasa rayukansu sakamakon karancin cimaka a jihar Nassarawa da ke Najeriya.

Jami'ar Kula da Cimaka ta Jihar Nassarawa Hajiya Halima Yusuf ta shaida cewa, akwai yara kanana dubu 5 da ke fama da matsalar karancin abinci a jihar.

Ta ce, a asibitocin jihar daban-daban akwai yara sama da dubu 2 da ake kula da su, kuma 81 daga cikin su sun rasa rayukansu.

Ta ce, sun fara hada kai da gwamnati da Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross don yaki da karancin cimakar.

Sakamakon hare-haren Boko Haram yara kanana kusan miliyan 35 ne ba sa samun isasshen abinci a Najeriya.


News Source:   ()