Karan farko tun bayan juyin mulki, hafsan hafsoshin Najeriya na ziyara a Nijar

Karan farko tun bayan juyin mulki, hafsan hafsoshin Najeriya na ziyara a Nijar

A lokacin wannan ziyara, Janar Christopher ya gana da takwaransa na Jamhuriyar Nijar Janar Moussa Salaou Barmou, inda bayanai ke cewa ɓangarorin biyu na tattaunawa ne a game da muhimman batutuwa da suka shafi a tsaro musamman a kan iyakokinsu.

Wannan ne dai karo na farko da wani babban jami’in gwamnatin Najeriya ya ziyarci ƙasar Nijar tun bayan kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya ƙarkashin jagorancin shugaba Mohamed Bazoum.

Bayan wannan juyin mulki, alaƙa ta yi tsami tsakanin sojojin da suka ƙwaci mulki da kuma ƙasashen Yankin Afirka ta Yamma musamman Najeriya, wadda ke jagorantar ƙungiyar Ecowas.

To sai dai lura da cewa akwai iyaka mai tsawon sama da kilomita dubu 1 da 500 tsakanin ƙasashen biyu da ke bai wa al’ummomi damar yin mu’amala da kuma ƙalubale musamman a ɓangaren tsaro, manazarta na ganin cewa akwai buƙatar kyautata alaƙa musamman ta fannin tsaro tsakanin Najeriya da Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)