Kanar Assimi Goita ya kori Firaminista da gwamnati

Kanar Assimi Goita ya kori Firaminista da gwamnati

Kasar Mali mai fama da rikicin kungiyoyin masu da’awar jihadi da ‘yan aware, sojoji sun karbi iko tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekara ta 2020 da 2021. Choguel Kokalla Maiga, wanda sojoji suka nada bayan juyin mulki na biyu, ya kasance wani mutum da ake kalo a matsayin  mai kima  aidanun yan kasar  ganin ta yada ya soki lamirin manyan kasashen Duniya da ke kokarin ci gaba da mulki bawa da ubangida,sai ga shi ranar Laraba Choguel Kokalla Maiga ya furta wasu kalamai da suka janyo suka daga ciki da wajen kasar musaman ga masu goyon bayan sojoji. Babban sakataren fadar shugaban kasa, Alfousseyni Diawara, ne ya karanta sanarwar sallamar Choguel Kokalla Maiga da gwamnati a gidan talabijin na kasar ORTM.

Tsohon Firaministan kasar Mali Choguel Maïga, a birnin  New York Tsohon Firaministan kasar Mali Choguel Maïga, a birnin New York © KENA BETANCUR / AFP

 Wasu jiga-jigan gwamnatin mulkin soja irinsu ministan tsaro Janar Sadio Camara da ministan sulhunta Janar Ismael Wague na cikin gwamnati. A watan Yunin 2022, gwamnatin mulkin sojan ta yi alkawarin shirya zabe tare da mika mulki ga farar hula a karshen watan Maris din 2024, amma daga baya ta dage zaben har abada.

Tsohon Firaministan Mali Choguel Kokalla Maiga a ranar Asabar ya fito fili ya yi Allah-wadai da rashin fayyace game da kawo karshen mulkin farar hula. Ya ce rudanin na iya haifar da "mummunan kalubale da kuma hadarin komawa baya". Maiga, mai shekaru 66, ya taba rike mukamin minista a lokuta da dama kuma ya tsaya takara sau uku a matsayin dan takarar shugaban kasa. Ya kasance fuskar farar hula na ginshiƙin dabarun mulkin soja daga tsohuwar mulkin mallaka na Faransa da kuma kusancin dangantakar siyasa da soja da Rasha.

RFI Afrique / Carte pays : Mali et sa capitale Bamako. Taswirar kasar Mali © FMM Studio graphique

 A Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumbar 2021, Maiga ya yi tir da abin da ya kira "watse a tsakiyar iska" dangane da sanarwar janye dakarun Faransa da ke yaki da masu da’awar jihadi.

Choguel Kokalla Maiga ya ce janyewar ta tilastawa kasar Mali ta binciko sabbin hanyoyi da sauran kawayenta, a daidai lokacin da kungiyar Wagner ta Rasha ta shiga cikin mawuyacin hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)