A wanan karon kamfanin ya shigar da karar ne a gaban cibiyar warware sabani da zuba jari da ake kira CIRDI inda yake neman a biyashi diyya daidai da asarar da ya tafka a mahakar Somair
Matakin dai na zuwa ne, bayan korar karar da Orano ya shigar kan gwamnatin Nijar a watan Disamban 2024 kan zargin kwace masa lasisin hako makamashin Uranuim a mahakar Imouraren, guda daga cikin rijiyoyi mafi girma a duniya.
Orano ya ce dabaibayin da gwamnatin Nijar ta yi masa, musamman a harakar kasuwancin ma’adinin da ya ke hakowa ya jefa mahakar Somair cikin mumunan yanayin rashin kudi tare da haddasa masa asara mai tarin yawa.
Rahotanni sun nuna cewa wannan itace hanya daya tilo da ta rage wa Orano domin a bi masa hakokinsa, bayan da ya gaza cimma nasara ta hanyoyin sulhu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI